Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba da jajircewar Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da kuma yadda ya jawo wa Najeriya martaba da kima a idon duniya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a sakon taya murnar cika shekara 63 a duniya da ya aike wa Mista Jonathan din.
- Ba za mu taba bari Najeriya ta ruguje ba —Buhari
- Na ga wulakanci a Gwamnatin Buhari —Zainab Buba Galadima
“Shugaba Buhari ya jinjina daukaka mai ban mamaki wadda ba kasafai akan ga irinta ba a fagen siyasar Najeriya da tsohon shugaban kasar ya samu, da kuma jajircewarsa wadda ta ba shi damar aiki a baya-bayan nan a matsayin manzon kungiyar ECOWAS na musamman wajen dawo da zaman lafiya a Jamhuriyar Mali”, inji sakon mai dauke da sa-hannun Hadimin Shugaban Kasa kan Watsa Labarai, Femi Adesina.
A ranar Juma’a ne Mista Jonathan, wanda Buhari ya gada a mulki a 2015. ke cika she 63 da haihuwa.
Ya yi addu’a Allah Ya ba wa tsohon shugaban karin hikima, da lafiya da tsawon kwana mai albarka domin ci gaba da hidimta wa al’umma.