Tsohon Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Dakta Doyin Okupe, ya rasu.
Dakta Doyin Okupe ya rasu ne a asibiti a Legas, bayan fama da jinya a sakamakon cutar kansa.
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da rasuwar Doyin Okupe ta wata sanarwa a safiyar Juma’a.
Doyin Okupe wanda ya rasu yana da shekara 72, gwamnan ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.