Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata tattaunawar sirri da Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo a fadarsa da ke Abuja ranar Lahadi.
Babu wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar a kan ganawar, amma mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Watsa Labarai, Femi Adesina ya wallafa wasu hotuna da safiyar Litinin na shugabannin biyu shafinsa na Facebook.
- Rufe shagunan ‘yan Najeriya a Ghana tsana ne
- Koro ‘yan Najeriya: Za mu sa kafar wando daya da Ghana – Lai Mohammed
Ko a makon jiya sai da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya wakilci Buharin a taron musamman na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) a birnin Accra na kasar ta Ghana kan rikita-rikitar siyasar kasar Mali.
A ’yan watannin baya dai an samu takun saka tsakanin kasashen biyu bayan rusa wani sashe na ginin ofishin jakadancin Najeriya a Ghana da kuma rufe shagunan wasu ’yan Najeriya a kasar.
Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da cewa mutanen da abin ya shafa an kwato musu hakkokinsu daga hukumomin kasar.
Ya ce, “Mun yi ta tattaunawa kai tsaye tsakanin Shugaba Buhari da Shugaba Akufo-Addo inda muka yi masa korafi a hukumance. Hukumomin kasar sun yi mana alakwarin sake bude shagunan har karo uku, amma abin mamaki har yanzu ba su bude ba.
“Ina tunanin dole mu kara matsa kaimi wajen tabbatar da cewa sun yi abin da ya kamata”, inji Osinbajo.
Daga nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya kan su ci gaba da bin doka, yana mai tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba kasashen biyu za su warware sabanin.
Rahotanni kuma sun tabbatar da cewa Mataimakin Shugaban Kasar ya kewaya ofishin jakadancin da ake zargin wasu fusatattun ’yan Ghana sun rusa kusan kaso 80 cikin 100 na ginin.