✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Nijar halartar taron ECOWAS

Taron zai tattauna kan rikicin Mali, yaki da COVID-19 da kuma kudin ECOWAS

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin domin halartar taron Shugabannin Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) kan yaki da cutar coronavirus.

A watan Afrilu kungiyar ta ECOWAS ta nada Shugaba Buhari a matsayin shugaban kwamitinta na yaki da cutar, wanda zai gabatar da rahoto a taron na yini guda.

Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar, Malam Garba Shehu, ya ce Buhari zai jagoranci yakar annobar cutar coronavirus a Yammacin Afirka.

Zauren Shugabannin ECOWA ya kuma zabi ministocin Najeriya na lafiya da sufurin jiragen sama da na kudi a matsayin shugabannin kwamitocin da suka shafi ma’aikatunsu, wanda Buhari zai jagoranta domin samun nasara a yaki da coronavirus.

Taron zai kuma karbi rahoto a kan samar da takardar kudin bai-daya na ECOWAS daga Julius Midara na kasar Saliyo da kwamitinsa.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Jean Claude Kassi Bou, zai gabatar wa taron rahoton wucin gadi a kan Muradun ECOWAS na shekarar 2050 da sauransu.

Sauran batutuwan da taron zai tattauna sun hada da karuwar matsalar tsaro a yankin da kuma rikicin siyasar kasar Mali.