Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Jihar Bauchi domin ziyarar aiki na kwana biyu.
Gwamnan Jihar Bauchi Muhammed Abubakar da takwaransa na Jihar Adamawa da wasu ministoci suna cikin wadanda suka tarbi shugaban a filin jirgin Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.