✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya sallami ministan noma da na lantarki

Sabo Nanono da Mamman Saleh sun rasa mukamansu a ranar Laraba.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya sallami Minsitan Noma, Sabo Nanono da takwaransa na wutar lantarki, Mamman Saleh daga mukamansu.

Bayan ya sallami ministocin biyu a ranar Laraba, Shugaban Kasar ya maye gurbinsu da Ministan Muhalli, Mohammed Mahmoud Abubakar da kuma Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Abubakar Aliyu.

Hadimin Shugaban Kasa, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a Fadar Shugaban Kasa ranar Laraba.

Nan gaba ne dai ake sa ran Fadar Shugaban Kasa za ta sanar da sunayen mutanen za su cike gurabun ministocin da aka sallama.

Karin labarin na tafe.