✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sabunta rajistarsa a jam’iyyar APC

Buhari ya sabunta rajistar a mazabarsa ta Sarkin Yara da ke garin Daura.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake sabunta rajistarsa ta jam’iyyar APC a mazabarsa ta Sarkin Yara da ke garin Daura a Jihar Katsina.

Tawagar wasu kusoshin jam’iyyar ne suka yi rakiyar shugaban kasar a ranar Asabar ciki har da wasu gwamnonin jam’iyyar da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne Shugaban Kasar ya koma cibiyarsa ta garin Daura domin hawa sahun sabunta rajista a jam’iyyarsa ta APC.

Wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasar Malam Garba Shehu ya fitar ta ce, Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da Mataimakinsa da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da kuma Babban Alkalin Jihar ne suka tarbe shi a Filin Jiragen Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke birnin Dikko.

Daga nan Buhari ya hau helikwafta ya karasa zuwa mahaifarsa da ke Daura, inda a nan kuma Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya jagoranci hakimansa wajen tarbar sa.

Sanarwar ta ce ana sa ran komawarsa Abuja a ranar Talata.