Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a fito da hatsi da yawansa ya kai metric ton dubu arba’in daga rumbunanta a raba wa ’yan Najeriya domin kawo saukin tsadar kayan abincin da ya addabi kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin da nufin rage radadin tsadar kayan abinci musamman a watan Ramadan da ake ciki da kuma lokacin bukukuwan Sallah da na Ista suke kara matsowa.
- ’Yan bindiga sun harbe dagaci yana sallah a masallaci a Taraba
- Dattawan Arewa sun bukaci Buhari ya yi murabus saboda matsalar tsaro
“Daga cikin hatsin akwai kason da za mu ba wa Ma’aikatan Agaji da Ayyukan Jin Kai, ta raba wa jama’a,” a cewar Ministan Ayyukan Gona da Raya Karkara, Mohammed Abubakar.
Ministan, wanda Shugaba Buhari ya gayyata domin jin bahasin halin da ake ciki daga bakinsa, ya bayyana cewa Ma’aikatan Agaji da Ayyukan Jin Kai, za ta samu Metric ton dubu goma sha biyu daga cikin metric ton 40,000 da za a fito da shi daga rumbun hatsin gwamnati domin raba wa ’yan Najeriya masu karamin.