Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar karbo sabon bashin Naira biliyan 850 saboda gudanar da wasu aikace-aikace a cikin kasafin kudi na shekarar 2020.
Buhari ya mika bukatar hakan ne a wani sako da ya aike wa Majalisar Dattawa wadda shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta a zamanta na ranar Talata.
A sakon, Buhari ya bukaci majalisar ta bai wa gwamnati damar tattaro bashin a cikin gida saboda gudanar da aikace-aikacen.
Sakon dai bai ba da bayani a kan aikace-aikacen da za a gudanar ba.
Shugaban majalisar ya umarci kwamitinta na kudi da ya yi aiki tare da Ministar Kudi saboda samo cikakkun bayanai a kan bashin.