Shugaba Muhammadu Buhari ya nada kwamitin da zai zauna a teburin sulhu da Twitter domin tattauna sabanin da ya kai ga an dakatar da amfani da shafin a Najeriya.
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin watsa labarai, Segun Adeyemi ya fitar a ranar Talata ta ce, an nada kwamitin ne bayan da kamfanin Twitter ya aike da wani rubutaccen sako na neman sasanci da gwamnatin kasar.
- Da dumi-dumi: NLC za ta ci gaba da yajin aiki a Kaduna
- An kashe dan bindiga yana kokarin sace mutane
Sanarwar ta ce kwamitin ya kunshi Ministan Sadarwa; Isa Pantami, Ministan Shari’a; Abubakar Malami, Ministan Harkokin Waje; Geoffery Onyeama.
Sauran yan kwamitin sun hada Ministan Ayyuka da Gidaje; Babatunde Fashola, Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka; Dokta Chris Ngige da wasu wakilai daga hukumomin gwamnati.
Makonni biyu da suka gabata ne Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed wanda zai jagoranci kwamitin sasancin, ya ce an dakatar da Twitter ne saboda yadda yake bayar da dama ga wadanda ke barazana ga wanzuwar Najeriya a matsayin kasa dunkulalliya.