✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya mika wa sanatoci kasafin 2021 zuwa 2023

Shugaba Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta aminta da kasafin kudin na shekarar 2021 zuwa 2023, wato “Medium Term Expenditure Framework and Fiscal Strategy Paper”.…

Shugaba Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta aminta da kasafin kudin na shekarar 2021 zuwa 2023, wato “Medium Term Expenditure Framework and Fiscal Strategy Paper”.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da Shugaba Buhari ya hado da kundin kasafin a zauren Majalisar, ranar Talata.

Shi dai kasafin kudin na matsakaicin zango na kunshe ne da ayyukan da gwamnati ke son ta gudanar wadanda za su amfanii rayuwar al’ummar kasa.

“Ina farin cikin turo tsarin kasafin kudi na matsakaicin zangon 2021 – 2023 domin wannan majalisa mai daraja ta duba ta kuma aminta da shi”, kamar yadda ya rubuta a wasikar.

Ya kuma yaba wa Majalissar kan goyon bayan da ta ba shi wajen gudanar da mulkinsa musamman maido da lokacin kasafin kudi daga Janairu zuwa Disamba.

Ya ce sun yi iya kokarisu na ganin sun gabatar da kundin 2021–2023 MTEF/FSP don bai wa yan Majalisar isasshen lokacin gudanar da aikinsu.

Ya kuma ce, aiwatar da kasafin kudin na bana ya dogara ne a kan amincewa kan kundin da ya gabatar musu, don haka ya nemi goyon bayansu na gaggauta aiwatar da abin da ya dace.

Majalissar Dattawa ta kuma kara karbar wata bukatar da Buhari ya turu don aminta da Dakta Chukwuemeka Chukwu, a matsayin Kwamishinan Zabe mai wakilta Jihar Abiya.