✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya mika wa majalisa sunan sabbin alkalai 11

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen sabbin alkalai 11 da zai nada a Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke zamanta a…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen sabbin alkalai 11 da zai nada a Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke zamanta a Abuja.

Buhari ya sanar da majalisar ne ta cikin sakonsa da Shugaban Majalisar Ahmed Lawan ya karanta wa takwarorinsa a zamansu na ranar Talata.

“Kamar yadda Sashe na 256(2) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya yi tanadi, ina neman amincewar Majalisa da sunayen nan guda 11 a matsayin Alkalai a Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja”, inji wasikar.

Sabbin wandanda za a nada din da jihohin da suka fito su ne:

 • Abubakar Husseini Musa (Adamawa).
 • Edward Okpe (Binuwai).
 • Babashani Abubakar (Borno).
 • Emuesiri Francis (Delta).
 • Jude Ogho (Delta).
 • Josephine Enobi (Edo).
 • Christopher Opeyemi Oba (Ekiti).
 • Mohammed Idris (Kano).
 • Hassan Maryam Aliyu (Kebbi).
 • Fashola Akeem Adebowale (Legas).
 • Da kuma Hamza Muazu (Neja).