✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya koma Daura don yin rajistar APC

Ranar Talata ake sa ran komawarsa Abuja.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina domin  bin sahu a aikin yin rajista a jam’iyyarsa ta APC.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da Mataimakinsa da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar da kuma Babban Alkalin Jihar ne suka tarbe shi a Filin Jiragen Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina.

Daga nan Buhari ya hau helikwafta ya karasa zuwa mahaifarsa da ke Daura, inda a nan kuma Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya jagoranci hakimansa wajen tarbar sa.

Daga cikin abubuwan da Buharin zai yi a Dauran akwai yin rajista da sabunta rajistar ‘ya jam’iyyar APC.

Ana sa ran komawarsa Abuja ranar Talata.