Gwamntin Tarayya ta kashe Naira tiliyan 2.8 wurin aiwatar da manyan ayyuka a shekarar 2020.
Ministar Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a yayin kaddamar da kasafin kudin 2021 a Abuja ranar Talata.
- Ganduje zai ba Kwankwaso sarautar mahaifinsa
- Duk wanda ya saki matarsa ko da a shirin fim ne ta saku — Dokta Bashir
- Dangote ya tafka asarar Naira biliyan 342 a cikin sa’o’i 24
Da take bayani a taron da aka gudanar ta bidiyo, Ministar ta ce kashi 89% na kudaden an kashe su ne a kan manyan ayyuka.
Sai dai ta yi bayani cewa Naira biliyan 118.3 kuma an kashe su ne a kan manyan ayyukan yaki da annobar COVID-19.
Ta ce a shekarar 2020, Najeriya ta kashe tiriliyan N3.27 wurin biyan basuka, sai kuma tiriliyan N3.19 da aka kashe wurin biyan albashi da fansho a shekarar ta 2020.