Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama matasan sojoji 10 da suka kammala samun horo a matakin farko a makarantar koyon tukin jirgin sama ta kasa da kasa da ke Enugu.
Shugaban kasar ya karrama matukan jirgin ne yayin bude bikin taron Babban hafsan sojoji na shekarar 2017 wanda aka yi a garin Ibadan da ke jihar Oyo,a jiya.