Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da kasafin kudin 2020 da aka yiwa kwaskwarima ga Majalisar Dokoki ta Kasa don neman amincewarta.
Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin Majalisar Dattawa Sanata Babajide Omoworare ne ya mika kundin ga Shugaban Majalisar, Sanata Ahmad Lawan.
An dai yi kwaskwarima ga kasafin kudin ne bayan da farashin mai ya fadi a kasuwannin duniya sakamakon barkewar annobar coronavirus.
- Amincewa da kasafin kudin badi da wuri zai kawo saukin rayuwa?
- Kasafin Kudi: Za a kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya Naira Biliyan 2.3
Wata majiya da ba ta so a fadi sunanta a Majalisar Dattawan ta ce Sanata Ahmad Lawan ya umarci Kwamitin Kudi a karkashin jagorancin Sanata Barau I. Jibrin ya fara aiki a kan kundin nan take.
An kuma ruwaito cewa kwamitocin majalisar masu ruwa da tsaki a lamarin za su fara tuntubar ministocin da abin ya shafa ranar Alhamis a kan kundin.