Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Jamhuriyyar Nijar domin halartar Taron Shugabannin Kasashen Kungiyar Rayya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS).
Buhari wanda ke jagorantar Kwamitin Yaki da annobar coronavirus na Majalisar Shugabannin Kasashen ECOWAS, zai gabatar da rahoton kwamitinsa a zaman na ranar Litinin, a binin Niamey na Jamahuriyar Niyar.
- Tarihi ba zai manta da Buhari ba kan cire tallafin kaya a Najeriya
- Yaki da COVID-19 na barazanar dawo da cutar Shan-inna
Taron wanda shi ne karo na 57 zai kuma tattauna kan batun yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a yankin da kuma rikicin shugabancin kasar Mali inda sojoji suka yi juyin mulki.
Buhari ne ke jagorantar kokarin samar da sasanci a rikicin na Mali, wanda Kungiyar ECOWAS ta nada tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan a matsayin Babban Mai Shiga Tsakani.
Sauran batutuwan da zaman zai tattauna sun hada da rahoto kwamitinsa kan samar da takardar kudi ta bai-dayan a yankin na Yammacin Afirka.
Sai kuma rahoton aiwatar da Muradun ECOWAS na shekarar 2050 da za a gabatar a zaman taron.
Buhari zai dawo Najeriya da zarar an kammala taron na kwana daya.