Shugaba Muhammadu Buhari jiya ya kaddamar da kwamitin bin diddigin dukiyoyin sace da kuma wadanda aka kwato a ciki da wajen Najeriya.
Membobin kwamitin sun hada da Olufemi Jinadu da Chinyere Bibiogha da kuma Mohammad Nami.
Buhari ya ce gwamnatinsa ta rika bin kudaden da aka sace tare da kwato illahirin dukiyoyin da aka sace a wajen Najeriya ta hanyar yin amfani da doka da kuma diflomasiyya.