Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin Bunkasa Tattalin Arziki na Fasahar Intanet a Najeriya.
Aminiya ta ruwaio cewa, Shugaba Buhari ya kaddamar da wannan shirin ne ranar Juma’a a Fadar Gwamnatin Najeriya.
- Kotu ta yanke wa mutum 3 hukuncin rataya a Ondo
- Ranar Dimokuradiyya: Gwamnati ta ba da hutun yini guda
Ministan Sadarwar da Tattalin Arziki ta Fasaha, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, shi zai jagoranci kwamitin shirin mai mambobi 27 a madadin Shugaba Buhari.
Buhari ya kaddamar kwamitin da zai jibinci wannan aiki ta hanyar ribatar fasahar Intanet wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da kaimi a fanin fasahar intanet domin samun ribar fasahar zamani domin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Mambobin Kwamitin sun hada da Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya; Muhammad Inuwa Yahaya, Gwamnan Jihar Gombe; Nasir Ahmed El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna; Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa; Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Jihar Legas da Sanata Hope Uzodinma, Gwamnan Jihar Imo.
Sauran sun hada da Dakta Zainab Shamsuna Ahmed, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare; Otunba Richard Adeniyi Adebayo, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari; Dokta Folasade Yemi-Esan, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya; Farfesa Umar G. Danbatta, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya; Farfesa M.B Abubakar, Manajan Darakta na Kamfanin Galaxy Backbone Limited; Dokta. Abimbola Alale, Manajan Darakta na Hukumar Kula da Fasahar Tauraron Dan Adam, da Engr Aliyu A. Aziz, Darakta Janar, Hukumar Bayar da Shaidar Dan Kasa.
Haka kuma a cikin kwamitin akwai Mista Oswald Osaretin Guobadia, Babban Mataimakin Na Musamman Ga Shugaban Kasa Kan Bunkasa Fasaha; Engr Olufemi Olufeko, Darakta Sashen Kula Da Fasaha a Ma’aikatar Sadarwa; A.B. Okauru, Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin Najeriya; Farfesa Simon Adesina Sodiya; Shugaban Kungiyar Masana Kwamfuta a Najeriya da Gbenga Adebayo, Shugaban Kungiyar Kamfanonin Sadarwa Masu Lasisi a Najeriya (ALTON).
Sauran mambobin sun hada da Farfesa Kabiru Bala, Wakilin Malamai kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya; Farfesa Nnenna Oti, Wakilin Jami’ar Fasaha kuma Mataimakin Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri da Kashifu Inuwa Abdullahi, Sakatare Janar kuma Shugaba na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa.
Kazalika, akwai Mista Sungil Son, Daraktan na KOICA), Dokta Olufemi Adeluyi, Mataimaki na Musamman Wajen Kula da Harkoki Fasaha a Fannin Bincike da Ci gaba ga Ministan Sadarwa da Abubakar A. Dahiru, Mataimaki na Musamman Wajen Kula da Inganta Tsaro ta Intanet ga Ministan Sadarwa.