Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yi wa albashi garambawul inda ya bukaci membobin kwamitin su cimma matsaya kan karancin albashin ma’aikatan kasar.
Kwamitin wanda ya kunshi mutum 30 ya na karkashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikatan Najeriya, Ama Pepple.
An yi bikin kaddamarwar a dakin taron na fadar shugaban kasa a Abuja jiya.