Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah kan yadda take bayar da gudunmawa wajen bunkasa ilimi, da kuma yadda kungiyar take yi wa gwamnati da kasar nan addu’o’in alheri tare da bayar shawarwari kan yadda za a inganta tafiyar da gwamnati.
Shugaba Buhari wanda shi ne Babban Bako na Musamman a wajen babban taron kungiyar na shekara-shekara tare da wa’azi da kuma kaddamar da gidauniyar bunkasa ilimi da ayyukan kungiyar da aka gudanar a a tsohon filin Fareti da ke Abuja a ranar Asabar da Lahadi ya bayyana haka ne ta bakin wakilinsa Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Sheikh Isa Ali Pantami, inda ya yi godiya ga kungiyar da kuma yi mata fatar alheri.
Shugaban ya bayar da gudunmawar miliyoyin Naira ga kungiyar a matsayin gudummuwarsa ta kashin kansa, sai dai ya ce kada a bayyana adadin kudin. Kungiyar ta kaddamar da asusun neman taimakon Naira miliyan 285 don gina karin manya da kananan makarantu da kayan aiki kamar motoci da sauran kayayyakin ofis domin bunkasa ilimin addinin Musulunci da na zamani a sassan kasar nan.
Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, wanda shi kansa ya bayar da gudummawar Naira dubu 300, ya ce kawo yanzu kungiyar ta gina makarantu fiye da dubu hudu a fadin Najeriya, kuma wannan gidauniyar da aka kaddamar na da nufin fadada ayyukan ilimi ne.
An dai tara miliyoyin Naira a yayin wannan taro daga daidaikun mutane da gwamnatocin jihohi.
Daga ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar wanda yaaiko da gudunmawar Naira miliyan biyar
Taron ya samu halartar dubban jama’a daga sassan Najeriya.