✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya jajanta wa Kwankwaso, ya taya Ganduje murna

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dangane da rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwao, Hakimin Madobi.…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dangane da rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwao, Hakimin Madobi.

Cikin sanarwar da Shugaban Kasar ya fitar a ranar Juma’a, ya ce mutuwar Alhaji Musa Saleh rashi ne ga Najeriya baki daya kasancewarsa daya daga cikin tsofaffi kuma mafi kyawun sarakunan gargajiya a kasar nan.

Sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa Mallam Garba Shehu ya fitar, ya ce gudunmuwar da Marigayi Alhaji Musa Saleh ya bayar wajen samar da zaman lafiya da hadin kan al’umma, “ba za a manta da shi ba har bayan rasuwarsa.”

A cewar Shugaban Kasar, “Marigayi Saleh mutum ne mai kirkin gaske wanda ya dabi’antu da tawali’u da sauki kai kuma hakan ya sanya ya yi fice a cikin al’umma.”

Ya ce, “bari na yi amfani da wannan dama na mika ta’aziyata ga tsohon Gwamna Kwankwaso da Gwamnatin Jihar Kano, da kuma Masarautar Kano dangane da wannan babban rashi.”

“Allah Ya gafarta masa kuma Ya yi masa kyakkyawan sakamako da Gidan Aljannah,” inji Shugaban Kasar.

Kazalika, cikin wata sanarwar da fadar Shugaban kasar ta fitar a ranar Juma’a, Shugaba Buhari ya taya Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, murnar cika shekaru 71 a duniya.

Shugaban Kasar cikin wani sako na fatan alheri zuwa ga Ganduje da iyalansa ya ce, “Muna taya Gwamna Ganduje murna zagayowar ranar haihuwarsa. Allah ya kara ma lafiya da tsawon rai domin ka ci gaba da hidimta wa al’ummar Jihar Kano da kasar baki daya.”