✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da Tinubu da Akande

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu da jigo a jam’iyyar, Bisi Akande.   Taron wanda suka…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu da jigo a jam’iyyar, Bisi Akande.
 
Taron wanda suka yi shi cikin sirri ya gudana ne a cikin gidan shugaban kasa da ke cikin fadarsa da ke Abuja, jiya.
 
Sun dauki awonni suna gudanar da taron jim kadan bayan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci Buharin kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.