A ci gaba da fafutukar neman wanda zai zame wa dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC, Bola Tinubu Mataimaki, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawar sirri tare da Gwamnonin APC.
An gudanar da tattaunawar ce ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- Za a soma bincike kan kone ‘barawon babur’ a Bauchi
- An yi garkuwa da matar shugaban Jam’iyyar APC a Neja
Shugaban kungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ne ya jagoranci takwarorin nasa zuwa wajen Buhari.
Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin jam’iyyar ke ta fadi-tashin tsayar da wanda zai yi wa dan takararta Mataimaki a babban zaben 2023.
Mahalarta taron sun hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Gwamna Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa, Abdullahi Sule na Nasarawa, Simon Lalong na Filato, Yahaya Bello na Kogi da kuma Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo.
Bayanai sun nuna Bola Tinubu ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ne a matsayin wanda zai yi masa Mataimaki saboda rawar da ya taka wajen yakin neman zabensa.
Aminiya ta tattaro cewa, wasu ’yan jam’iyyar CPC, jam’iyyar da ta ba da gudunmawa wajen kafa APC, na shirin ganawa da Shugaba Buhari domin ba da shawara kan ko a zabi Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ko kuma Ministan Sufurin Jirgen Sama, Hadi Sirika a matsayin Mataimakin Tinubun.
Kazalika, shi ma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babagana Kingibe, wanda ya yi wa marigayi MKO Abiola takarar Mataimaki a zaben 1993 ya mika wa Gwamnan Atiku na Jihar Kebbi, wasu sunaye guda uku don ya mika wa Tinubun ya zabi mutum guda daga ciki don su yi takara tare.
Sunayen da Kingibe ya mika din su ne na; Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Mohammed da kuma tsojon jami’in hulda na Majalisar Tarayya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, Kashim Ibrahim-Imam.
Sai dai duka wadanda lamarin ya shafa baki dayansu Musulmai ne daga shiyyar Arewa maso Gabas.
Kuma mika sunayen ya biyo bayan korafin da aka yi ne kan cewa APC na shirin tsayar da Musulmai a matsayin ’yan takararta.
Lamarin da aka ce bai yi wa Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da kuma wasu masu ruwa-da-tsaki na APC dadi ba.