Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan hutun mako biyu da ya tafi kasar Birtaniya domin ganin likita a birnin London.
A ranar 30 ga watan Maris Shugaban Kasar ya tashi daga Abuja zuwa London, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
- Ganduje da Dantata sun sasanta Dangote da BUA
- Pantami ya ce a ci gaba da sayar da sabbin layin waya
- Wacce ta fi kowa tsawon farata a duniya ta yanke su
- ’Yan bindiga sun kai hari dab da barikin soja da ke Jaji
Saukar Buhari a Filin Jirgi na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a yammacin Alhamis, tamkar ba-zata ce ga wasu ’yan Najeriya da ke shirin yi masa zanga-zanga a London a ranar Asabar.
A lokacin tafiyar tasa, wasu ’yan Najeriya sun gudanar zanga-zangar adawa da goyon baya a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke London.
Wasu daga cikinsu na zarginsa da nuna halin ko-in-kula game da halin da bangaren lafiya ke ciki a kasar.
Hakan kuma ya zo ne a yayin da ake kai ruwa rana tsakanin gwamnati da likitoci masu barazanar zuwa yajin aiki saboda rashin biyan su hakkokinsu.