✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya bai wa Ministan Ilimi mako 2 ya kawo karshen yajin aikin ASUU

Buhari ya umarci Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya kasance daga mahalarta zaman tattaunawar sulhu da gwamnati ta kira malaman jami'ar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu, mako biyu ya kawo karshen yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke yi.

Ya umarci Ministan da ya jagoranci zaman sulhun da gwamnati ta gayyaci ASUU domin sasantawa da ita da sauran kungiyoyin jami’o’i da ke yajin aiki.

Ya kuma ba shi wa’adin mako biyu ya tabbata ya shawo kan duk matsalolin da suka hana sulhu da malaman jami’ar, sannan a kawo mishi rahoto.

Karin bayani na tafe…