Shuagaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi masu yunkurin neman a kara mishi wa’adin mulki su daina, yana mai cewa a kai kasuwa, shi ba shi da bukata.
Buhari ya ce sauran wata 18 da suka rage masa sun ishe shi kuma zai yi kokarin cika duk alkawuran da ya dauka kafin karewar wa’adin mulkinsa.
- Babban taro: Hukuncin kotu ya jefa PDP cikin halin rashin tabbas
- Wane dalili ya sa aka yi ‘keyboard’ a hargitse?
Shugaban ya yi wannan jan kunne ne a lokacin da ya gana da ’yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya bayan ya halarci taron zuba jari sannan ya yi Umrah.
“Na yi rantsuwa da Alkur’ani cewa zan gudanar da mulkina yadda kundin tsarin mulki ya tanada kuma zan sauka idan lokacina ya kare, to don haka babu zancen tazarce a shekarar 2023,” inji shi.
Ya kara da cewa baya son wani ya kara masa wa’adin yana mai cewa ko an kara masa wa’adin ma ba zai karba ba.
A karshe Buhari ya yi kira da yan ’yan Najeriyar mazauna Saudiyyar da su zama yan kasa na gari masu bin doka da kuma kauce wa duk wani da zai zubar da kimarsu a duk inda suka tsinci kansu.