✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ce a rage farashin kayan abinci

Ya ce ya damu da tsadar abinci ya kuma umarci a fito da abinci daga rumbun gwamnati

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta dauki kwararan matakan da za su kai ga rage farashin kayan masarufi a fadin Najeriya.

Shugaban ya bayar da umarnin fitar da fitar da kayan abinci daga rumbun gwamani ciki har da ton 30,000 domin samar da abinci a kasa da saukaka wa masu noman kaji.

Buhari ya bayyana damuwa game da hauhawar farashin kayan abinci a kasar, wadda tattalin arzikinta ke fama da matsi sakamakon annobar coronavirus.

Ya kuma ce gwamantinsa na tattaunawa da kuniyoyin masu samar da kayan abinci musamman na shinkafa da sauran nau’ika hatsi domin samun sauki.

Ya ce samun hadin kansu zai taimaka kuma nan ba da jimawa ba farashin zai sauka.

Ya bayyana haka ne a sakon da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar, na juyayin asarar da aka yi a iftila’in ambaliyar ruwa a fadin kasar nan.

Buhari ya ce ambaliyar da ta mamaye gonaki na yi barazana ga samuwar wadataccen abinci Najeriya.

Ya bayyan cewa a Jihar Kebbi kadai gonakin da ambaliya ta mamaye sun kai fadin hekta 500,000 kuma an yi asarar amfanin gona na sama da Naira biliyan biyar.