✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci wasu jami’ai su kaurace wa Villa

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan jaridar da ke daukar rahoto a Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock Villa su…

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan jaridar da ke daukar rahoto a Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock Villa su killace kansu su yi aiki daga gida na kwanaki 14.

Jami’an dai su ne suka halarci sallar jana’iza  da kuma binne Malam Abba Kyari, Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati Attah Eesa ne ya sanar da hakan, inda ya ce umarnin yin hakan wani matakin riga-kafi ne da aka dauka.

Abba Kyari ya rasu ne ranar Juma’a a wani asibiti da ke Legas bayan ya kamu da cutar coronavirus, an kuma binne shi ranar Asabar.

Bayan binne Abba Kyari, masana kiwon lafiya da kuma wasu ’yan Najeriya sun bukaci  duk wadanda suka halarci jana’izar su killace kansu, saboda sun yi watsi da umarnin da jami’an kiwon lafiya suka bayar na barin tazara da wasu sharudda da suka gindaya don kare kansu daga cutar coronavirus.

Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa a kan Harkar Yada Labarai Malam Garba Shehu, wanda ke cikin wadandasuka halarci jana’izar, ya ce babu wani bakon abu a wannan matakin da aka bukace su dauka, kamar yadda wallafa a shafinsa na twitter.

“Hakan ya dace da sharuddan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) da Ma’aikatar Lafiya suka gindaya. Ana yin haka ne don hana yaduwar cutar coronabvirus”, inji shi.

Sauran jami’an da suka halarci jana’izar sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a Kan Harkar Tsaro Babagana Monguno, da Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami, da Ministan Aikin Gona Mustapha Baba Shehuri, da tsohon Babban Sakataren Gidan Gwamnati Jalal Arabi, tsohon Gwamnan Borno Kashim Shettima, da sauransu.