✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya bayyana manyan ayyuka 3 da ya kaddamar a ranar Talata

Shugaba Muhammadu Buhayi ya sanar da cewa gwamnatinsa ta kaddamar da wasu manyan ayyuka uku da za ta aiwatar. A wani sako da Shugaban kasar…

Shugaba Muhammadu Buhayi ya sanar da cewa gwamnatinsa ta kaddamar da wasu manyan ayyuka uku da za ta aiwatar.

A wani sako da Shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ayyuka da ya kaddamar za su hada da aikin shimfida sabon layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

Sauran ayyukan da Shugaban ya kaddamar sun hada da tashar jirgin ruwa ta Bonny a Jihar Ribas da kuma babbar tashar jirgin kasa a birnin Fatakwal da za a rika jigilar kayayyakin da aka samar a cikin gida.

Kazalika, ya ce layin dogon da za a shimfida daga Fatakwal zuwa Maiduguri zai zama hanyar jigilar kayayyakin da aka samar sannan kuma za ta bunkasa sufurin cikin gida gami da shigowa da fitar da kaya zuwa ketare.