Gwamnatin Tarayya, a ranar Juma’a, ta bayar da gudummawar ton 360 na hatsi domin raba wa marasa galihu a Jihar Yobe.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da kayayyakin ga Gwamnatin Jihar Yobe a Damaturu, hedikwatar jihar.
Shugaba Buhari, wanda Mista Abubakar Aliyu ya wakilta, ya ce: “Na zo ne domin in isar da wannan sako na ton 360 ga Gwamnatin Jihar Yobe domin bai wa marasa galihu a fadin jihar.”
Da yake karbar hatsin, Gwamna Mai Mala Buni, ya yi godiya ga Gwamnatin Tarayya kan alfarmar da aka yi wa jihar na tallafin hatsi.
Buni, wanda mataimakinsa, Idi Gubana, ya wakilta, ya ce matakin zai taimaka wa kokarin gwamnatin jihar wajen bayar da tallafin jinkai domin inganta samar da abinci a jihar.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce an karbo kayayyakin cikin yanayi mai kyau.
Goje wanda Daraktan Ma’aikata na SEMA, Hassan Bomai ya wakilta, ya ce hukumar ta samu masara ton 210, gero ton 60, dawa ton 60, sai gari ton 30.
Sakataren na SEMA ya ba da tabbacin hukumar za ta yi iya kokarin ta wajen raba kayayyakin ga marasa galihu a jihar kamar yadda aka tsara da yardar Allah.