Shugaban Kasa Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da ba Jamhuriyar Nijar kyautar motocin da kimarsu ta haura Naira biliyan daya da don ta inganta harkokin tsaronta.
Rahotanni sun ce za a ba Nijar motocin kirar Toyota Land Cruiser guda 10 ne kamar yadda ta roki Najeriya, kodayake gwamnatin Najeriyar ba ta bayyana dalilin kyautar ba.
- Yunwa ba za ta sa mu janye yajin aiki ba — ASUU
- Rahoto kan ’yan bindiga: NBC ta ci tarar Trust TV miliyan 5
Da take amsa tambayoyin manema labarai a kan lamarin ranar Laraba, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta kare matsayin na gwamnati.
Ta ce Shugaba Buhari na da ikon yin kowacce irin kyauta a duk lokacin da ya ga dama, kuma wannan ba shi ne karon farko da Najeriya ke ba wasu kasashen tallafi ba.
Zainab ta ce, “Tsawon lokaci, Najeriya kan tallafawa makwabtanta musamman ma na kurkusa don su inganta sha’anin tsaronsu, kasancewar mu ma ya shafe mu.
“Wannan ba shi ne karon farko da Najeriya ke tallafa wa kasashen Nijar da Kamaru da Chadi ba.
“Shugaban Kasa yakan dubawa ya yi abin da ya dace daidai da bukatar shugabannin kasashen. Bayan an yi hakan mukan amince mu tallafa musu.
“Mun yi haka ne don mu tallafa musu. Hakika ’yan Najeriya na da damar su yi tambaya kan abin da ba su gamsu da shi ba, amma shi ma Shugaban Kasa yana da alhakin duba mene ne zai fi zamar wa kasar mafi a’ala, sannan ya zartar. Ko ni ba zan iya kalubalantar shi ba a kan haka,” inji Ministar.