Shugaba Buhari ya ba ministoci wa’adin mako guda kowannensu ya kawo rahoton tattaunawarsa da al’ummarsa kan rikicin da ya biyo bayan zanag-zangar #EndSARS.
Wa’adin da ya bayar dori ne a kan umarninsa na makon jiya cewa kowane minista ya koma mazabrsa ya tattauna na masu fada a ji domin kwantar da wutar rikicin.
“Biyu daga cikinsu ne rahotonsu ke kasa [a ranar Laraba] saboda har yanzu wasunsu na jihohinsu suna aiwatar da uamrnin na Shugaba Kasa.
“Saboda haka Shugaban Kasa ya bada umarnci cewa dole kowannensu ya mika wa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya rahotonsa a makon gobe”, a cewar Hadimin Shugaban kKasa kan Watsa Labarai, Femi Adesina.
Umarnin Buharin ta biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin sojoji da harbin masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Jihar Legas, da kuma yadda zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali da kashe-kashe da satar dukiyoyi a sassan Najeriya.
Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta ce sojoji sun kashe mutum 12 a wurare biyu a Jihar Legas a ranar da aka yi harbin Lekki.
Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin na Amnesty International a matsayin labarin kanzon kurege.