Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda.
Majalisar ta shawarce shi da ya yaki ’yan ta’addar gaba daya ta kowace hanya, har da yin luguden bama-bamai a kan maboyarsu don kawar da su daga ban kasa.
- Za a toshe layin sadarwa a Kaduna —El-Rufai
- Taurin bashi: Kamfanonin mai 77 sun rike wa gwamnati N2.7 tiriliyan
Zaman Majalisar na ranar Laraba ya kuma bukaci Shugaba Buhari da ya ayyana duk sanannun shugabannin ’yan bindiga a matsayin mutanen da ake nema ruwa a jallo, a bibiye su a duk inda suke don kamawa da gurfanar da su.
Shawarwarin sun biyo bayan kudirin da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir mai wakiltar Sakkwato ta Gabas da wasu takwas suka gabatar.
Gobir ya koka wa zauren Majalisar cewa yanzu yankin Gabashin Sakkwato ya zama mafakar ’yan bindiga saboda farmakin da ake kai musu a Jihar Zamfara.
Ya kuma nuna damuwa cewa yanzu akasarin ’yan ta’adda da ake kai wa farmaki sun koma kananan hukumomin Sabon Birni da Isa na Jihar Sakkwato saboda ragargazar da sojoji ke musu a Jihar Zamfara.
Ya ce yayin da ake ci gaba da fatattakar su daga Jihar Zamfara, babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka a Jihar Sakkwato, wanda hakan ya ba su damar mamaye wasu yankunan jihar.
A cewarsa, ba a tsara hare-haren da sojoji ke kai wa ’yan bindigar da kyau ba saboda a Zamfara kawai ake kai su, a maimakon dukkannin jahohin da ’yan ta’addan suka addaba.
Ya bayyana cewa ya kamata a fadada hare-haren, kuma a rika kaiwa a tare, maimakon a takaita a wuri daya ko lokuta daban-daban don samar da sakamako mai inganci.
Sanata Gobir ya ambato kisan jami’an tsaro 21 da ’yan bindiga suka yi a ranar Asabar da ta gabata a yankunan Dama da Gangara, duk da cewa har yanzu ba a iya tantance adadin fararen hula da aka kashe a kauyukan da ke makwabtaka da su ba.
Dan majalisar ya ce kisan kiyashin ya nuna girman matsalar, wadda ke bukatar hadin kai da daukar matakan gaggawa ta hanyar ayyana yakin da miyagun gaba daya.
Majalisar ta yi tsit na minti daya don karrama sojoji da fararen hula da suka rasa rayukansu a munanan hare-haren barayin dajin.
Zauren Majalisar ya kuma umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da sauran hukumomin Gwamnatin Tarayya da su gaggauta bayar da dukkan taimakon da ya dace ga wadanda harin ’yan ta’adda ya rutsa da su a Sakkwato da sauran sassan kasar nan.