Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da a biya kimanin Naira miliyan 164 na kudin makarantar ’yan matan Chibok 106 da ke karatu a jami’ar Amurka da ke garin Yola a cikin jihar Adamawa.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Harkokin Yada Labarai da Wayar Da Kan Jama’a, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata.