Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba ya yi zargin cewa rashin meman shawara ne ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza tafiyar da Najeriya yadda ya kamata.
Ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Trust TV, mallakin Media Trust.
- Zaben shugabannin APC: Tsintsiya na iya watsewa
- Abin da ya jawo rikicin shugabanci a Majalisar Malaman Kano —Sheikh Ibrahim Khalil
Ya ce a shekaru shidan da ya shafe yana mulki, Shugaban ya yi nesa da abubuwan da ke faruwa a zahiri, lamarin da ya ce ya jefa zargi tsakaninsa da ’yan Najeriya.
Tsohon Kakakin ya ce, “Ba zai yuwu ka rika tafiyar da kasa a yanayin da yake nuna kai ba ka jin shawara ba, kuma ba ka damu da mutane ba, in da ma ra’ayin ya yi daidai da bukatun mutane to da da sauki.”
Ghali Na’Abba ya ce hatta ’yan Arewa, wadanda daga nan ne Shugaban ya fito ba sa jin dadin mulkinsa.
“Yau a Arewa, mutane da dama na ganin cewa shekarun mulkin Buhari kamar asararsu aka yi, saboda bai tsinana musu komai ba, shi ya sa ma ba sa so mulki ya bar yankinsu.
“To amma wanne dalili ne ma zai sa a sake zaben dan Arewa a cikin irin wannan yanayin? Shi ne babban abin mamakin,” inji shi.
Tsohon Kakakin ya ce sabanin lokacin mulkin PDP da suke da kusoshi kimanin 30 da suke zama duk ranar Litinin su ba Shugaban Kasa shawara, Buhari ba ya tuntubar kowa.
Hakan a cewarsa shi ne ummul’aba’isun shiga halin da Najeriya ke ciki.