✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na neman ciyo bashin N22.7trn; Majalisa ta ki yarda

Tun da gwamnati ta fara samun gibi a kudaden shiga, ta koma dogaro da CBN don aiwatar da wasu manyan ayyuka

Majalisar Dattawa ta yi watsi da bukatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na sake fasalin rancen Naira Tiriliyan 22.7 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa Gwamnatin Tarayya.

Karkashin wani tsarin CBN, Gwamnatin Tarayya za ta iya rancen kudi a wajensa domin aiwatar da bukatun gaggawa, da kuma cike gibin kasafin kuɗi.

Sai dai tun da gwamnatin ta fara samun gibi a kudaden shiga, ta koma dogaro da CBN don aiwatar da wasu manyan ayyukan da dama.

A makon da ya gabata ne Buhari ya  bukaci majalisar ta yi gyaran fuska ga bashin CBN din da gwamnati ta riga ta karbo, don karo wasu kudade da yawansu ya kai N23.7trn da za ta biya a shekaru 40, da kuma sanya kashi 9 na kudin ruwa.

Sai dai hakan ya haifar da hayaniya a majalisar saboda rahoton da ya fito daga kwamitin kudin da ya nazarci bukatar shugaban kasar.

Hayaniyar ta fara ne lokacin da Sanata Betty Apiafy ta ce wannan tsarin na CBN ba sananne ba ne a dokar cike gurbin kasafi ta Najeriya.

Sai dai Shugaban Majalisar Ahmad Lawan ya ce ba ta da hurumin fatali da batun, gabanin gabatar da rahoton kwamitin a kansa.

Shi ma dai Sanata Thompson Sekibo ya ce bai amicne da bukatar ba, musamman idan aka yi la’akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulki, da na sashe na 38 na dokar CBN.

“Sashi na 38 na dokar CBN t’ya ce duk kudin da Gwamnatin Tarayya ta karba a matsayin bashi, sai ta biya su sannan take da ikon karbo wani,” in ji sanatan.

A don haka ya ce laifi ne rashin sanar da majalisar batun karbo bashin tunda fari kuma ba dalci ba ne majalisar a amince da wannan kudirin,” inji shi.

Kwamitin dai karkashin jagorancin Shugaban Masu Rinjaye, Ibrahim Gobir, zai gabatar da rahotonsa a ranar 17 ga Janairu, 2023 lokacin da Majalisar za ta dawo zamanta daga hutun sabuwar shekara.