Shugaba Buhari na jagorantar zaman Majalisar Tsaro ta Kasa, karo na uku a kasa da mako biyu.
Ana zaman ne baya makamantansa biyu da aka gudanar a baya-bayan nan, inda Shugaban Kasar ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ta dabaibaiye kasar, ya kuma bayyana aniyar suntakatattsa kai da fata.
A lokacin zaman Manyan Hafsoshin Tsaro da Shugaban ’Yan Sanda, Shugaban Hukumar Leken Asiri da Ministan Tsaro da sauransu za su yi wa Shugaban Kasar bayani game da inda aka kwana wajen magance matsalar da ke addabar kasar.
Sauran mahalarta zaman na ranar Talata su hada da Mashawarci kan Tsaron Kasa, sai kuma Ministan Shari’a Abubakara Malami, Ministan Harkokin Cikin Gida Ogbeni Rauf Aregbesola da Minstan Harkokin Waje Geoffrey Oyema.