✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari na ganawar sirri da Sarakuna

Shugaba Buhari na ganawar sirri tare da Sarkin Musulmi da wasu sarakuna a Fadar Gwamnati.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ganawar sirri da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III da wasu sarakuna a Fadarsa da ke Abuja.

Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Najeriya ya jagoraci sarakunan zuwa halartar zaman wanda ba a kai ga fayyace makasudinsa ba.

Sai dai ana ganin shugaban na ganawa da sarakunan ne domin jin shawarwarinsu kan yadda za a magance matsalolin Najeriya, duba da irin mummunan sakamakon da zanga-zangar #EndSARS ta haifar.

Sarakuna da ke halartar taron na ranar Alhamis sun hada da Sarkin Kano, Alhajij Aminu Ado Bayero; Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwushi; Sarkin Fika; Tor Tiv da Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Imo da sauransu.

Idan ba a manta ba a ranar 23 ga Oktoba, 2020, Buhari ya yi wata ganawa da tsoffin shugabannin kasa da suka hada da Janar Yakubu Gowon, Cif Olusegun Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Janar Abdulsalami Abubakar, Goodluck Jonathan da kuma Cif Earnest Shonekan.

Akwai ci gaban labarin.