✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na duba yiwuwar biyan tallafin mai na N6.7trn a 2023

Biyan tallafin mai na tiriliyan 6.7 a2023 na barazana ga kudaden da matakan gwamnati uku za su samu daga Asusun Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar kashe Naira tiriliyan 6.7 wajen biyan tallafin man fetur a shekarar 2023.

Kudin da za a kashe ya dara wanda aka ware a kasafin 2022 da Naira tiriliyan 2.53, a yayin da gwamnatin ta ce a watan Mayu take son daina biyan tallafin kwata-kwata.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa biyan tallafin da gwamnatin ke hasashe a 2023 na nufin watakila gwamnatoci a dukkan matakai uku ba za su samu ko sisi ba daga kudaden da Najeriya ke samu a bangaren mai.

Hakan kamu zai yi mummunan tasiri ta hanyar jawo nakasu ga kudaden da za a ware wa bangaren aiwatar da manyan ayyuka.

Idan haka ta faru, karshenta sai dai a kara ciyo bashi domin gudanar da ayyukan.

Sai dai Ministar Kudin ta yi bayani cewa mafita ita ce soke biyan tallafin man fetur daga watan Mayu na shekarar ta 2023.

Da take bayani kan Kundin Kasafi Mai Mastakaicin Zango (MTEF 2023-2025), Ministar ta bayyana cewa akwai hanyoyi biyu da za a iya  aiwatar da kasafin 2023:

Na farko shi ne: “Kamfanin NNPC ya biya tallafin fetur na tiriliyan N6.7 a 2023 a madadin Gwamnatin Tarayya.”

Sai dai ta ce idan aka yi hakan babu abun da zai rage na a zo a gani domin rabawa tsakanin matakai uku na gwamnati daga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Wannan raguwa da za a iya samu a kudaden da matakan gwamnatin za su raba zai yi illa ga yawancin gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi wajen aiwatar da ayyukansu.

Na biyu kuma, ta ce, shi ne: “A ci gaba da biyan tallafin zuwa karshen wa’adin wata 18 a watan Mayu, wanda shi kuma zai bukaci tiriliyan 3.36.

“Duk wanda aka dauka akwai tasiri da zai yi kan kudaden Asusun Gwamnatin Tarayya da kuma irin gibin da ake hasashe,” kamar yadda ministar ta bayyana.

Ta ce idan aka dauki zabi na farko, to kasafin zai kasance Naira tiriliyan 17, idan na biyun kuma aka zaba to zai zama tiriliyan 16.

A baya dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha nuna adawarsa ga janye tallafin man fetur, yan cewa janyewar san kara jefa talakawa cikin mastin rayuwa.

A ganinku wanne ne ya fi?

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Chris Agabi, Philip S. Clement & Simon E. Sunday