Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojojin kasar da su yi amfani da karfi wajen murkushe ’yan bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a Jihar Neja.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce shugaban ya bayar da umarnin ne ga hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ).
Sanarwar ta ce, “A matsayinsa na babban kwamandan sojojin Najeriya, shugaban kasa ya shirya kulla damarar gagarumin farmakin soji a Jihar Neja wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga da ’yan Boko Haram da ke tserewa daga Arewa maso Yamma, da kuma Arewa maso Gabashin kasar nan.”
A sakonsa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja kuwa shugaban ya ce “Ina mika sakon ta’aziyya da alhini a gareku, sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan.”
Shugaba Buhari ya nanata cewa samar da tsaro nauyi da rataya a wuya kowace alumma kuma ta hanyar bai wa hukumomin tsaro hadin kai ne za a iya kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Ya ci gaba da cewa “A shirye gwamnatin tarayya take ta karfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukkan jihohin. Na yi imanin cewa tare da cikakken hadin kan ’yan kasa, tabbas za mu shawo kan wannan matsala,” in ji shugaban kasar.
A Talatar makon jiya cewa akalla mutum 13 suka rasa rayukansu a sakamakon wani hari da ’yan bindiga suka kai da tsakar rana a kauyukan Nakundna da Wurukuchi da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Wannan hari dai na zuwa ne bayan aukuwar makamacinsa cikin kasa da makonni biyu wanda ’yan bindiga suka kai wa ma’aikata a Madatsar Ruwa ta Zungeru, inda suka kashe mutum biyu sannan suka yi awon gaba da wasu ’yan kasar China uku.