Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce babu wanda ya taɓa girmama marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi bayan rasuwarsa.
Shugaba Tinubu, ya ayyana ranar jana’izar Buhari a matsayin hutu na ƙasa.
- Muna binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki — EFCC
- AGILE: ’Yan mata 40,630 za su samu tallafin karatu a Yobe
Haka kuma, ya halarci jana’izar marigayin da kansa, ya gana da iyalan Buhari, ya gudanar da taron majalisar zartarwa (FEC) domin girmama shi.
Sannan ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno, domin tunawa da Buhari.
Shehu Sani, ya ce waɗannan abubuwa da Tinubu, ya yi abin koyi ne.
“Shugaban ƙasa, ya halarci jana’izar Buhari da kansa, ya gana da iyalansa, ya ayyana hutu na ƙasa, ya gudanar da taron majalisar zartarwa don girmama shi, sannan ya sauya sunan jami’a domin tunawa da shi,” in ji Shehu Sani a shafinsa na X.
“Wannan girmamawa ce da marigayi Buhari bai taɓa yi wa wani ba. Amma sai aka ce wai yana amfani da rasuwar Buhari ne don samun karɓuwa.
“Me za su ce da bai yi komai daga cikin waɗannan ba? Siyasa dai abu ne mai ban mamaki.”
Wannan saƙon nasa ya sa sama da mutum 1,000 sun goyi bayansa zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, sai dai rubutun nasa ya jawo cece-kuce.
Maganganun Shehu Sani sun fito ne bayan jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar ADC, ta zargi gwamnatin Tinubu da amfani da mutuwar Buhari don neman farin jini.
Amma mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ƙaryata waɗannan zarge-zargen.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta yi abin da ya dace cikin girmamawa da mutunci.
“Wasu mutane sun fitar da sanarwa suna zargin cewa gwamnatin Tinubu tana amfani da mutuwar Buhari don neman karɓuwa. Wannan zargi ba gaskiya ba ne,” in ji Dare.
“Kuma abin kunya ne ga miliyoyin ’yan Najeriya da suka yi jimamin mutuwar Buhari, kuma suka ga yadda aka gudanar da jana’izarsa cikin mutunci da girmamawa.”
Ya ce an gudanar da jana’izar Buhari cikin mutunci, kuma manyan baƙi daga ƙasashen duniya sun halarta, yayin da miliyoyin mutane suka kalla ta kafafen yaɗa labarai.
“Shugaba Tinubu ba ya neman farin jini a banza,” Dare ya kara da cewa.
“Ayyukansa na ci gaba ne za su yi masa jagoranci, ba irin surutun da jam’iyyu marasa tasiri irin su ADC ke yi ba.”
Cece-kuce na ci gaba da kaurewa a kafafen sada zumunta, yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da yadda aka girmama Buhari bayan rasuwarsa.