A yau Litinin ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar nana a zaben 209. Hakan ya sa wasu suka fara tofa albarkacin bakinsu.
Jigo a jam’iyyar PDP, Femi Fani Kayode ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba zai yi nasara ba a zaben shekarar 2019 kamar yadda Daily Nigerian suka kalato daga shafinsa na Twitter.
A cewarsa, “mutumin bai da wata abin nunawa baicin zubar da jinni da mutuwa da cin hanci da raba kan al’umma ne wai zai sake tsayawa takara. Ba zai yi nasara,” inji shi.