Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa tashar jirgin kasa mafi girma a hanyar Itakpe zuwa Warri sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ne ya sanar da haka ranar Asabar, yayin da yake duba aikin layin dogon da ya ce nan gaba zai karasa Abuja.
“An sa wa tashar sunan Goodluck Jonathan kuma shugaban kasa ya amince”, inji Ameachi, wanda ya bayyana gamsuwa da ingancin aikin.
“Idan ka ga aiki mai inganci babu bukatar tambaya. Kyamarar ka ma za ta shaida maka cewa wannan aiki nagari ne, wannan tashar jirgi ta Goodluck Jonathan da ke Agbor ce”, inji ministan.
Rashin kula da kayan gwamnati
Sai dai kuma ya bayyana damuwa kan dabi’ar rashin kulawa da kayan gwamnati musamman a wurin magada.
“Daga baya ne za mu gane ko hukumar NRC mai kula sufurin jiragen kasa ta san aikinta, domin matsalar ita na wajen kula da kaya.
“Na ga bayikan sun yi kyau kwarai, amma ba na fata in dawo nan bayan shekara hudu ko biyar in iske duk ya lalace, domin na ga na Kubwa duk sun gaji.
“Idan wani abu ya lalace a sauya shi kawai. Yana da kyau mu koyi dabi’ar kula da kayan da muka gada a hannun wasu”, inji minstan.