✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bugun zuciya ya kashe kanin Maradona

Marigayin shi ne dan autan namiji a gidansu Maradona.

Hugo Maradona, kanin Diego Maradona kuma tsohon dan wasan kwallon kafa ya rasu yana da shekaru 52.

Kulob din Italiya Ascoli ya ce ya mutu yau Talata a gidansa da ke Monte di Procida, kusa da Naples, sakamakon bugun zuciya.

Hugo ya mutu ya bar ’ya’ya uku da matarsa, Paola Morra wadda ya aura a shekarar 2016.

Marigayin shi ne dan autan namiji a gidansu Maradona, inda yana da wasu ’yan uwan mazan biyu – Diego da Raul.

Napoli ta sayi kanin Maradona a shekarar 1987 bisa rokon Diego aka ba da aronsa ga Ascoli.

Ya kuma buga wasa a Rayo Vallecano, Rapid Vienna da sauran kungiyoyi da dama a duniya.

Mutuwar Hugo ta zo ne watanni 13 bayan Diego Maradona ya mutu sakamakon bugun zuciya yana da shekaru 60 wanda ajali ya katse masa hanzari makonni biyu bayan da aka yi masa tiyata a kwakwalwa.

“Shugaban kulob din Aurelio De Laurentiis, mataimakin shugaban kasa Edoardo De Laurentiis, jami’ai, ma’aikatan horarwa, ’yan wasa da dukan dangin SSC Napoli suna jimamin rashin, tare da dangin Maradona bayan mutuwar Hugo,” in ji Napoli.