Matar da fitaccen dan jaridar Washington Post da aka yi wa kisan gilla, Jamal Khashoggi zai aura, Hatice Cengiz, ta yi karar Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman a gaban wata kotu a Amurka, kan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar.
Cengiz tare da wata kungiyar kare hakkin dan Adam da Khashoggin ya kafa gabanin na karar yariman da ake wa lakabi da MBS tare da wasu ’yan Saudiyyar fiye da 12, suna neman diyyar kisan gillar da aka yi masa a Istanbul a 2018.
Karar da suka shigar ranar Talata a wata kotu da ke Washington, na zargin an kitsa kashe Khashoggin ne a Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Washington, babban birnin Amurka, inda ya je neman takardun da za su ba shi damar auren Cengiz.
Takardar karar ta ce MBS da jami’an da ta ambata sun “fara aiwatar da shirin kawar da Mista Khashoggi ta hanyar kisan gillar ne a bazarar 2018’’.
Takardar na zargin an kistsa makircin ne bayan MBS jami’an kasar sun yi zargin Kashoggi na neman kawo sauyin dimokuradiyya a Saudiya ta hanyar amfani da kungiyar tasa mai rajin kawo tsarin dimokuradiyya a yankin Larabawa (DAWN).
Ta ce wadanda ake zargin sun yi amfani da bukatar mamacin ta yadda ofishin jakadancin da ke Washington ya shaida masa cewa dole sai ya je ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, Turkiyya, kafin ya samu takardun da yake bukata.
Ta ce wadanda ake zargin “sun karkatar da Mista Khashoggi ne domin kawo cikas a fafutikar siyasar da yake yi daga Amurka ta yadda za su samu damar kawar da shi”.
An dai kashe Khashoggin cikin ofishin na Istanbul ranar 2 ga watan Oktoban 2018, kuma har yanzu ba a ga gawarsa ba.
Saudiyyar ta amince jami’anta ne suka yi wa dan jaridan kisan gilla, amma ta ce ba da sanin MBS aka aiwatar da danyen aikin ba.
An soki batun kisan gillar a kasashen duniya da dama, inda ’Yan Majalisar kasar Amurka suka gabatar da kudurin dokar da ta zargi MBS da hannu a kisan.
A Turkiya kuma, Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya sha nanata cewa lallai sai ya hukunta masu hannu a kisan.
Karar da budurwar tasa Misis Cengiz da kungiyar da ya kafa, DAWN, tana neman a biya diyyar kudi, wanda suka ce kotun ce kawai take da hakkin yanke hukunci a kai.
“Ina cike da fatar za mu samar wa Jamal adalci da gaskiya a wannan karar da muka shigar.
“Na yi amanna da tsarin shari’ar Amurka wajen sauraron abin da ya faru daki-daki tare da hukunta masu hannu a wannan mummunan aikin”, inji Cengiz a bayanin da ta gabatar.