✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta halaka kanta da maganin kwari a Jega

Wata budurwa mai kimanin shekara 15 mai suna Khadija Chindo ta halaka kanta ta hanyar shan maganin kwari sakamakon wata karamar takaddama da iyayyenta a…

Wata budurwa mai kimanin shekara 15 mai suna Khadija Chindo ta halaka kanta ta hanyar shan maganin kwari sakamakon wata karamar takaddama da iyayyenta a Jega da ke Jihar Kebbi.
Wata majiya ta kusa da iyalan marigayiyar ta ce lamarin ya auku ne a ranar Litinin da ta gabata da yamma bayan takaddama da innarta da kuma mahaifiyarta a Sabon Gari da ke Jega.
“Mahaifiyarta Fatima wadda suka rabu da mahaifinta ta yi mata fada lokacin da ta ji labarin ta yi fada da innarta. Ita ma innarta wadda take zaune a gidansu ita ma aurenta ya kare da nata mijin. Ta yi barazanar za ta kashe kanta idan iyayenta suka ci gaba da yi mata fada kan laifin da ta yi. Daga baya sai ta shanye wata karamar kwalba ta maganin kwari da ake kira piya-piya, inda ta rasu da daddare kuma aka yi jana’izarta washegari Talata da safe a Jega.”
Sheikh Rimi Jega wanda ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar lamarin, ya bayyana hakan a matsayin abin takaici da ya saba wa Musulunci.
Ya ce, “Iyayenta suna zaune ne a Unguwar Rimi kafin su koma Sabon Gari, iyaye ne masu matukar mutunci. Ban san me ya same ta ta kashe kanta ba. A Musulunci duk wanda ya kashe kansa Annabi Muhammad (SAW) ya ce wuta ce makomarsa. Don haka ina mamakin abin da ya faru da wannan yarinyar za ta halaka kanta.”
Ya kara da cewa, “Wannan ya nuna budurwar ba ta samu kyakkyawar tarbiyya daga mahaifanta ba. don haka ina shawartar iyaye su rika kokarin tabbatar da kyakkyyawar dangantaka a tsakaninsu da ’ya’yansu kuma su rika lura da duk wani sauyin hali da suka gani daga gare su.  
Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin ’yan sanda ya ci tura. Kuma kiran waya da sakon tes da aka aika wa Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi Sylbester Ome da Kakakin Runduna, DSP Muhammad Mainagge ba su mayar da amsa ba har zuwa hada wannan rahoto.