✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta banka wa masoyinta wuta don ya ki aurenta

Ta kulle shi da mahaifiyarsa a daki sannan ta cinna musu wuta

Wata budurwa ta cinna wa masoyinta wuta a cikin dakinsa bayan ya dakatar da shirye-shiryen aurensa da ita.

Da misalin karfe 1:30 daren Talata budurwa ta yi yunkurin babbake masoyin nata da mahaifiyarsa da wanin karamin yaro a gidansa da ke Layin Shaahu a Karamar Hukumar Gboko, Jihar Binuwai.

Budurwar ta yi aika-aikan ne saboda masoyin nata da suka dauki tsawon lokaci suna caba soyayya ya ki amincewa da aurenta bayan sun samu sabani.

Makwabta sun shaida wa Aminiya cewa saurayin ya dakatar da shirin aurensa da masoyiyar tasa ce saboda munanan halayenta ga uwarsa.

Hakan ce a cewarsu, ta sa dangantakar da ke tsakaninsu ta yi tsami har saurayin ya ce budurwar ta kwace kayanta ta bar gidansa.

Wani ganau ya ce bayan da saurayin ya umarci budurwar ta bar gidan hayan da take zaune da shi, sai da masoyan suka yi awanni suna rikici.

Da ta tafi sai ta dawo cikin tsakar dare tare da wasu maza uku, ta sa kwado ta kulle gidan ta waje, ta yago wani gidan sauron sannan ta zuba masa fetur sannan ta cinna wa gidan wuta.

Shaidu sun ce saurayin ya ce ya lokacin da ta yago gidan sauron ta zuba masa fetur ta jefa a gidan da shi da mahaifiyarsa da karamin yaron suke, sannan ta kyasta ashana ta jefa kafin ta hau babur din sa suka zo da shi suka tsere.

Makwabta sun ce kururuwar saurayin da mahaifiyarsa da karamin yaron ce ta taimaka aka kawo musu dauki aka kubutar da su a kan lokaci.

Mazauna yankin sun ce mahaifiyar saurayin da karamin yaron sun samu kananan kuna daga gobarar amma shin nashi kunar na da tsanani.

Jami’ar Hulda da Jama’ar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar a daren Talata.

Ta ce bayan masoyan suka yi fada, budurwar ta yi wa saurayin barazana, amma ta ce ba a rasa rai ba duk da cewa saurayin ya samu mummunan rauni.

DSP Catherin ta kara da cewa har yanzu ba a kame kowa ba saboda budurwar da ake zargi da aikata laifin ta tsere.