✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude makarantu: Malamai za su shiga yajin aiki

Jihohi su cika matakan kariyar COVID-19 a makarantu ko su hakura da malamai

Malaman makarantun firamare da sakandare a Najeriya na barazanar shiga yajin aiki a daidai lokacin da ake shirin bude makarantun.

Shugaban Kungiyar Malamai ta Kasa (NUT) Nasir Abubakar ya ce malamai a fadin kasar ba za su koma koyarwa ba har sai gwamnatocin jihohi sun cike sharudda da matakan kariyar COVID-19.

Ya bayyana haka ne da yake jawabi game da shirin sake bude makarantu bayan wata shida da rufe su saboda bullar cutar ta COVID-19 a Najeriya.

Shugaban na NUT ya ce malamai da dalibai da yawa musamman a yankunan karkara sun kamu da cutar saboda rashin cikakken bin matakan kare yaduwar cutar.

Idan ba a manta ba Gwamnatin Tarayya ta umarci makarantu a dukkannin matakai da su fara shirin komawa aji ta hanyar samar da abubuwan kariya, duk da cewa ba ta ayyana ranar komawar ba.

A watan Maris ne Najeriya ta rufe makarantu, ‘yan makonni bayan bullar cutar COVID-19, da zummar takaita yaduwar cutar.