✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude filin wasa na Akwa Ibom: Yau Pele zai kawo ziyara Najeriya

A yau Juma’a 7 ga watan Nuwamba ne ake sa ran bude sabon filin wasa na Jihar Akwa-Ibom. Daga cikin manyan bakin da aka gayyato…

A yau Juma’a 7 ga watan Nuwamba ne ake sa ran bude sabon filin wasa na Jihar Akwa-Ibom.

Daga cikin manyan bakin da aka gayyato akwai shahararren dan kwallon Brazil Pele da kuma wasu daga sassan duniya. Haka kuma ana sa ran halartar Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a wajen bikin bude filin wasan.
A yau ne kuma ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles za ta fafata da ta kasar Ghana watau Black Stars a wasan sada zumunta a yayin bikin budewar.
Sannan wadanda suka shirya bikin sun tabbatar za a gudanar da kade-kade da raye-raye na al’adun gargajiya musamman wadanda suka fito daga Jihar Akwa Ibom.
Filin wasan, wanda zai rika daukar ’yan kallo kimanin dubu 30, an bayyana shi a matsayin wanda babu kamarsa a halin yanzu a duk yankin Afirka ta Yamma. Ana kwatanta shi da filin wasa na Afirka ta Kudu wanda ake ganin a da babu mai kyansa a duk fadin Afirka.
Ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles za ta yi wasanta na karshe da kasar Afirka ta Kudu a gasar neman hayewa cin kofin Afirka wanda za a yi a ranar 19 ga wannan wata da muke ciki a filin wasan na Akwa Ibom.